Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Hadaya ta Gari

1. A sa'ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban.

2. Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

3. Ragowar garin hadayar kuwa, zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadaya ce ta ƙonawa mafi tsarki ga Ubangiji.

4. Sa'ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai.

5. Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai.

6. Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.

7. Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai.

8. Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa'ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden.

9. Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

10. Ragowar hadayar garin zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadayar ƙonawa ce mafi tsarki ga Ubangiji.

11. A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.

12. Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi.

13. Sai a sa gishiri a kowace hadaya ta gari, kada a rasa sa gishirin alkawarin Allah a hadaya ta gari. A sa gishiri a dukan hadayu.

14. Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza.

15. Za a zuba masa mai, a barbaɗa masa lubban, gama hadaya ce ta gari.

16. Firist kuwa zai ƙone wani kashi daga cikin ɓarzajjen hatsin a gauraye da man, da dukan lubban don tunawa, gama hadaya ce ta ƙonawa ga Ubangiji.