Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 19:23-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da 'ya'ya na ci, 'ya'yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba.

24. A shekara ta huɗu 'ya'yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji.

25. Amma a shekara ta biyar, sai ku ci 'ya'yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.

26. “Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri.

27. Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu,

28. ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.

29. “Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.

30. Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.

31. “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

32. “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.

33. “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.

Karanta cikakken babi L. Fir 19