Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 16:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa.

12. Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen.

13. Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu.

14. Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.

15. Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.

16. Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra'ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu.

17. Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita.

Karanta cikakken babi L. Fir 16