Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 16:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar 'ya'yan Haruna, maza biyu, sa'ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu.

2. Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.

3. Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.”

4. Sa'an nan Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa'an nan ya sa su.

5. Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama'ar Isra'ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa.

6. Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa.

7. Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

8. Sa'an nan ya jefa kuri'a kan bunsuran nan biyu. Kuri'a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel.

9. A wanda kuri'ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji.

10. Amma a wanda kuri'ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.

Karanta cikakken babi L. Fir 16