Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 15:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka.

14. A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.

15. Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16. Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17. Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

18. Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice.

19. Sa'ad da mace take haila irin ta ka'ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice.

20. Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

21. Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

Karanta cikakken babi L. Fir 15