Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 11:37-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba.

38. Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.

39. Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.

40. Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.

41. Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba,

42. duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa.

43. Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa.

44. Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.

45. Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.

46. Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu.

47. Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.

Karanta cikakken babi L. Fir 11