Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 28:24-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da ɓarawo yake.

25. Mutum mai haɗama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai sami wadar zuci.

26. Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.

27. Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la'ance shi.

28. Mutane sukan ɓuya sa'ad da mugaye suka sami iko, amma sa'ad da iko ya fita daga hannunsu adalai sukan ƙaru.

Karanta cikakken babi K. Mag 28