Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 28:20-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka sami dukiya dare ɗaya, za a hukunta ka.

21. Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.

22. Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.

23. Wanda ya tsauta wa mutum zai sami yabo daga baya, fiye da wanda ya yi masa daɗin baki.

24. Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da ɓarawo yake.

25. Mutum mai haɗama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai sami wadar zuci.

26. Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.

27. Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la'ance shi.

Karanta cikakken babi K. Mag 28