Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 26:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo bai dace da wawa ba, kamar yadda dusar ƙanƙara ba ta dace da lokacin zafi ba, ko ruwan sama a lokacin girbi.

2. La'ana ba za ta kama ka ba, sai dai in ka cancance ta. Tana kamar tsuntsayen da suke firiya da dare ba za su sauka ba.

3. Sai ka fyaɗi doki, ka sa wa jaki linzami, wawa kuma sai ka doke shi.

4. Idan ka amsa tambayar wauta, ka zama wawa daidai da mutumin da ya yi tambayar.

5. Ka amsa wauta ga tambayar wauta, wanda ya yi tambayar zai gane wawancinsa.

6. Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.

7. Wawa yakan yi amfani da karin magana kamar yadda tauyayyen mutum yake amfani da ƙafafunsa.

8. Wanda ya yabi wawa yana kama da wanda ya ɗaura dutse a majajjawa.

9. Karin magana a bakin wawa kamar sukar ƙaya ce a hannun mai maye.

10. Wanda ya ɗauki wawa aiki yana cutar duk wanda aikin ya shafa.

11. Wawan da yake maimaita aikin wautarsa yana kama da kare mai yin amai ya koma ya tanɗe.

Karanta cikakken babi K. Mag 26