Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 24:11-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi.

12. Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.

13. Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka,

14. haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.

15. Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce ƙwace, ko ka ƙwace masa gidansa, wannan mugunta ce.

16. Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.

17. Kada ka yi murna sa'ad da bala'i ya aukar wa maƙiyinka.

18. Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba.

19. Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.

20. Gama mugun mutum ba shi da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.

21. Ɗana, ka yi tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar kome da mutanen da suka tayar musu.

22. Irin waɗannan mutane sukan hallaka farat ɗaya. Ka taɓa yin tunani a kan bala'in da Allah ko sarki sukan aukar?

23. Masu hikima kuma sun faɗi waɗannan abu.Kuskure ne alƙali ya yi son zuciya.

24. Idan ya kuɓutar da mugu, kowane mutum da yake a duniya zai la'anta shi ya ƙi shi.

25. Alƙalan da suke hukunta wa mai laifi kuwa, za su arzuta, su ji daɗin kyakkyawan suna.

Karanta cikakken babi K. Mag 24