Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 23:23-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu.

24. Mahaifin adali yana da dalilin yin murna. Zai yi fāriya a kan ɗa mai hikima.

25. Ka sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi fāriya da kai, ka sa mahaifiyarka farin ciki.

26. Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali.

27. Karuwa, da mata mazinata, tarkon mutuwa ne su.

28. Sukan laɓe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci.

29. Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido?

30. Sai riƙaƙƙen mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi.

31. Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa'ad da kake motsa shi.

32. Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka.

33. Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba.

34. Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na ɗibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangaɗi.

35. Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”

Karanta cikakken babi K. Mag 23