Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 20:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.

5. Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.

6. Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.

7. 'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.

8. Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.

9. Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?

10. Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.

Karanta cikakken babi K. Mag 20