Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 19:15-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.

16. Ka kiyaye umarnai za ka rayu, in ka ƙi binsu kuwa za ka mutu.

17. Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.

18. Ka yi wa 'ya'yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.

19. Idan mutum mai zafin rai ne, ƙyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau ɗaya, sai ka sāke yi.

20. Ka saurari shawara, ka yarda ka koya, wata rana za ka zama mai hikima.

21. Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.

22. Abin kunya ne mutum ya zama mai haɗama, matalauci kuma ya fi maƙaryaci.

23. Ka yi tsoron Ubangiji za ka yi tsawon rai, ka kuma sami biyan bukata, ba abin da zai cuce ka.

24. Waɗansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa.

25. Za a hukunta mai fāriya saboda ya zama ishara ga mutanen da ba su san kome ba, mutum mai hikima yakan koya sa'ad da aka tsauta masa.

26. Sai marar kunya, marar mutunci suke wulakanta mahaifinsa, ko ya kori mahaifiyarsa daga gidansa.

27. Ɗana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya.

28. Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna ƙaunar yin mugunta.

29. Wawa mai fāriya hakika zai sha dūka.

Karanta cikakken babi K. Mag 19