Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 18:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da take daidai ba zai yarda ba.

2. Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya nuna kuzarinsa.

3. Zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncinka za ka sha ba'a a maimakonsa.

4. Harshen ɗan adam yana iya zama shi ne asalin hikima mai zurfi kamar teku, sabo kamar ruwan rafi mai gudu.

5. Ba daidai ba ne a yi wa mugun mutum alheri, sa'an nan a ƙi yi wa marar laifi adalci.

6. Sa'ad da wawa ya fara jayayya, yana neman dūka ne.

7. Sa'ad da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce, da ita ake kama shi.

8. Ɗanɗanar jita-jita daɗi gare ta, mukan ƙosa mu haɗiye ta.

9. Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.

10. Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.

11. Attajirai suna zato dukiyarsu ita ce za ta kiyaye su kamar garuka masu tsayi da suke kewaye da birni.

12. Ba wanda za a girmama sai mai tawali'u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.

13. Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.

14. Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa'ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.

Karanta cikakken babi K. Mag 18