Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 16:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.

5. Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.

6. Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.

7. Lokacin da ka yi abin da Ubangiji yake so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.

8. Gara ka sami kaɗan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba.

9. Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne yake bi da kai cikin ayyukanka.

10. Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.

11. Ubangiji yana son ma'aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.

Karanta cikakken babi K. Mag 16