Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 14:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.

6. Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.

7. Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.

8. Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.

9. Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.

10. Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.

11. Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.

Karanta cikakken babi K. Mag 14