Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 11:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.

22. Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.

23. Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun sami biyan bukatarsu kowa zai yi ɓacin rai.

24. Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.

25. Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.

26. Mutane sukan la'anci mai ɓoye hatsi, yana jira ya yi tsada, amma sukan yabi wanda yake sayar da nasa.

27. Idan nufe-nufenka na kirki ne za a girmama ka, amma idan kai mai neman tashin hankali ne, to, abin da zai same ka ke nan.

28. Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.

29. Mutumin da yake jawo wa iyalinsa wahala, ƙarshensa talaucewa. Wawaye za su zama barorin masu hikima a ko yaushe.

30. Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.

31. Idan an sāka wa mutumin kirki da alheri a duniya, hakika za a hukunta wa mugaye da masu zunubi.

Karanta cikakken babi K. Mag 11