Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 11:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.

11. Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.

12. Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.

13. Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.

14. Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.

15. Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.

16. Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.

17. In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.

18. A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da yake daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.

19. Mutumin da ya yi niyyar aikata abin da yake daidai zai rayu, amma mutumin da ya dukufa ga aikata mugunta zai mutu.

20. Ubangiji yana ƙin masu muguwar niyya, amma yana murna da waɗanda suke aikata abin da yake daidai!

21. Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.

22. Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.

23. Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun sami biyan bukatarsu kowa zai yi ɓacin rai.

Karanta cikakken babi K. Mag 11