Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 10:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Karin maganar Sulemanu ke nan. Ɗa mai hikima abin fāriya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

2. Abin da ka samu ta hanyar zamba ba zai yi albarka ba, amma gaskiya za ta cece ka.

3. Ubangiji ba zai bar mutumin kirki da yunwa ba, amma zai hana mugu ya kai ga biyan bukatarsa.

4. Ragwanci zai sa talauci, amma yin aiki sosai zai arzuta ka.

5. Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi.

6. Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.

7. Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.

8. Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.

9. Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.

10. Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama.

11. Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.

12. Ƙiyayya takan haddasa wahala, amma ƙauna takan ƙyale dukan laifofi.

Karanta cikakken babi K. Mag 10