Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 9:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”

7. Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”

8. Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.”Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?”

9. Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,

10. da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot.

11. Dattawanmu da dukan mazaunan ƙasarmu suka ce mana mu ɗauki guzuri a hannunmu don tafiya, mu tafi taryarku, mu ce muku, ‘Mu bayinku ne, yanzu dai sai ku yi mana alkawari.’

12. Wannan abinci, da ɗuminsa muka ɗauko shi daga gidajenmu a ranar da muka fito zuwa gare ku, amma ga shi, yanzu ya bushe ya yi fumfuna.

13. Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!”

14. Sai Isra'ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba.

15. Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu.

16. Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maƙwabtansu ne, suna zaune a cikinsu.

17. Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim.

Karanta cikakken babi Josh 9