Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 9:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.

19. Amma shugabanni suka ce wa dukan jama'a, “Mun riga mun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, don haka yanzu ba shi yiwuwa mu taɓa su.

20. Abin da za mu yi musu ke nan, a bar su da rai saboda rantsuwar da muka rantse musu don kada mu jawo wa kanmu fushin Ubangiji!”

21. Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.”

22. Joshuwa kuwa ya kirawo su, ya ce musu, “Me ya sa kuka ruɗe mu da cewa, ‘Muna nesa da ku ƙwarai,’ ga shi kuwa, a tsakiyarmu kuke zaune?

23. Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”

24. Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.

25. Yanzu dai muna a hannunka, ka yi yadda ka ga ya yi maka kyau.”

26. Haka kuwa ya yi musu, ya cece su daga hannun Isra'ilawa, har ba su kashe su ba.

27. Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

Karanta cikakken babi Josh 9