Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 6:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu.”

11. Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana.

12. Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.

13. Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙahoni bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, 'yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni.

14. A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa'an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida.

15. A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.

16. A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin.

17. Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.

18. Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa.

19. Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji.”

20. Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.

21. Sa'an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai.

22. Sa'an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, “Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata.”

23. Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa.

Karanta cikakken babi Josh 6