Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 6:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa.

2. Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka.

3. Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida.

4. Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.

5. Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”

6. Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, “Ɗauki akwatin alkawarin, sa'an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”

7. Ya kuma ce wa jama'a, “Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji.”

8. Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai waɗanda suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su.

9. Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni.

10. Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu.”

11. Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana.

12. Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.

Karanta cikakken babi Josh 6