Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 23:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra'ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa.

2. Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,

3. kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.

4. Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.

5. Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.

6. Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu,

7. domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.

Karanta cikakken babi Josh 23