Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 22:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.

17. Zunubin da aka yi a Feyor, ashe, bai ishe mu ba, har annoba ta wahalar da taron jama'ar Ubangiji? Ga shi, har yanzu ma ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba.

18. Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama'ar Isra'ila.

19. Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji inda alfarwa ta sujada take, ku sami abin mallaka a tsakaninmu, amma kada ku tayar wa Ubangiji, ku kuma tayar mana ta wurin gina wa kanku wani bagade dabam da bagaden Allahnmu.

20. Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra'ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.”

21. Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka amsa wa shugabannin iyalan Isra'ilawa suka ce,

Karanta cikakken babi Josh 22