Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 21:28-29-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28-29. Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin kabilar Issaka, biranen su ne, Kishiyon da wuraren kiwo nata, da Daberat da wuraren kiwo nata, da Yarmut da wuraren kiwo nata, da Enganim da wuraren kiwo nata.

30-31. Daga cikin rabon kabilar Ashiru aka ba su birane huɗu, su ne Mishal da wuraren kiwo nata, da Abdon da wuraren kiwo nata, da Helkat da wuraren kiwo nata, da Rehob da wuraren kiwo nata.

32. Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.

33. Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba iyalan Gershonawa guda goma sha uku ne.

34-35. Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata.

36-37. Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra'ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata.,

38-39. Daga cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata.

40. Dukan biranen da aka ba iyalan Merari na Lawiyawa guda goma sha biyu ne.

41. Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama'ar Isra'ila guda arba'in da takwas ne.

42. Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.

43. Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki.

44. Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko'ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu.

45. Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.

Karanta cikakken babi Josh 21