Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 21:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele'azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama'ar Isra'ila.

2. Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan'ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.”

3. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.

4. Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.

5. Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.

6. Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.

7. Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.

8. Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.

Karanta cikakken babi Josh 21