Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 19:23-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.

24. Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta.

25. Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf,

26. da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat.

27. Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul,

28. da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba.

29. Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib,

30. da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.

31. Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.

32. Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta.

33. Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun.

34. Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun.

35. Garuruwan da yake da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret,

36. da Adama, da Rama, da Hazor,

37. da Kedesh, da Edirai, da En-hazor,

38. da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.

Karanta cikakken babi Josh 19