Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 13:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.

7. Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”

8. Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,

9. daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,

10. da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa,

11. da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka,

12. da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su.

13. Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.

14. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.

Karanta cikakken babi Josh 13