Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 8:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’

2. Nemo mutum biyu amintattu, wato Uriya firist, da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama shaidu.”

3. Bayan wannan na yi jima'i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’

4. Kafin yaron ya isa kiran mama ko baba, Sarkin Assuriya zai kwashe dukan dukiyar Dimashƙu da dukan ganimar Samariya.”

5. Ubangiji kuma ya sāke yi mini magana.

6. Ya ce, “Saboda wannan jama'a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka,

7. ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa.

8. Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.”Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar .

9. Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!

10. Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.

11. Bisa ga ikonsa mai girma Ubangiji ya faɗakar da ni kada in bi hanyar da jama'ar ke bi. Ya ce,

12. “Kada ka haɗa kanka da jama'a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro.

13. Ka tuna fa, ni Ubangiji Mai Runduna, mai tsarki ne. Wajibi ne ni kaɗai za ka ji tsoro.

14. Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima.

15. Da yawa za su yi tuntuɓe su faɗi. Za su faɗi, a kuwa ragargaza su. Za a kama su da tarko.”

16. Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni.

Karanta cikakken babi Ish 8