Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 65:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu'o'in mutanena, amma ba su yi addu'a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al'ummar ba ta yi addu'a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’

2. Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu.

3. Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna.

4. Da dare sukan tafi cikin kogwanni da kaburbura, suna neman shawarar kurwar matattu. Waɗannan mutane sukan ci naman alade, su kuma sha romon naman da aka miƙa hadaya irin ta arna.

5. Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.

6. “Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari'ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu

7. saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”

8. Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da 'ya'yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini.

Karanta cikakken babi Ish 65