Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 56:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina.

2. Mai albarka ne mutumin da yake aikata wannan, da ɗan adam da yake riƙe da shi kam, wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ƙazantar da ita ba, wanda kuma ya tsame hannunsa daga aikata kowace irin mugunta.”

3. Kada baƙon da ya hada kansa da mutanen Ubangiji ya ce, hakika Ubangiji zai ware shi daga jama'arsa.Kada kuma baban ya ce shi busasshen itace ne.

4. Ga abin da Ubangiji ya ce, wa mutanen nan, “Ku babani waɗanda kuka kiyaye Asabar ɗina, ku da kuka zaɓi abubuwan da suka gamshe ni, kuka kuwa cika alkawarina da aminci,

5. zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na 'ya'ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”

Karanta cikakken babi Ish 56