Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 55:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi,Yanzu da yake kusa.

7. Bari mugaye su bar irin al'amuransu,Su sāke irin tunaninsu.Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu,Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.

8. Ubangiji ya ce,“Tunanina ba kamar irin naku ba ne,Al'amurana kuma dabam suke da naku.

9. Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,Haka al'amurana da tunanina suke nesa da naku.

10. “Maganata kamar dusar ƙanƙara take,Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.

11. To, haka maganar da na faɗa take,Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.

12. “Za ku fita daga cikin Babila da murna,Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama.Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa,Itatuwa za su yi ta sowa don murna!

13. Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa.Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada,Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”

Karanta cikakken babi Ish 55