Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 54:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.

9. “Na yi alkawari a zamanin Nuhu,Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba.Yanzu kuwa ina miki alkawari,Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba,Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.

10. Duwatsu da tuddai za su ragargaje,Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.Zan cika alkawarina na salama har abada.”Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.

Karanta cikakken babi Ish 54