Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 5:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.

9. Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.

10. Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”

11. Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa.

12. A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.

13. Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.

14. Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.

15. Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.

16. Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.

17. A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.

18. Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.

Karanta cikakken babi Ish 5