Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 48:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Amma duk da haka kuna fāriya, da cewaKu ne mazaunan birni mai tsarki,Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila,Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.

3. Ubangiji ya ce wa Isra'ila,“Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru,Sa'an nan na sa ya faru ba labari!

4. Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne,Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.

5. Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku,Na hurta abubuwa tun kafin su faru,Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su,Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.

6. “Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu,Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce.Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo,Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.

7. Yanzu ne kaɗai nake sawa su faru,Ba wani abu makamancin wannan da ya faru a baya.Da ya faru, da za ku ɗauka cewa kun san kome a kansa.

8. Na sani ba za a iya gaskata ku ba,Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa.Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan,Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.

9. “Saboda mutane su yi yabon sunanaShi ya sa nake danne fushina,Ina kuma ɓoye shi, kada in hallaka ku.

10. Na gwada ku da wutar wahala,Kamar yadda ake tace azurfa a tanda,Amma na tarar ba ku da amfani.

11. Abin da na yi, na yi shi don kaina ne,Ba zan bari a rasa girmama sunana ba,Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukakaWadda take tawa ce, ni kaɗai.”

12. “Ku kasa kunne gare ni, ya Isra'ila, jama'ar da na kira!Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!

13. Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya,Ya kuma shimfiɗa sammai.Lokacin da na kira duniya da sararin sama,Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!

Karanta cikakken babi Ish 48