Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 48:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Na gwada ku da wutar wahala,Kamar yadda ake tace azurfa a tanda,Amma na tarar ba ku da amfani.

11. Abin da na yi, na yi shi don kaina ne,Ba zan bari a rasa girmama sunana ba,Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukakaWadda take tawa ce, ni kaɗai.”

12. “Ku kasa kunne gare ni, ya Isra'ila, jama'ar da na kira!Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!

13. Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya,Ya kuma shimfiɗa sammai.Lokacin da na kira duniya da sararin sama,Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!

14. “Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne!Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba,Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila,Zai yi abin da na umarce shi.

15. Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi,Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.

Karanta cikakken babi Ish 48