Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 48:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila,Ku da kuke zuriyar Yahuza.Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji,Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila,Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.

2. Amma duk da haka kuna fāriya, da cewaKu ne mazaunan birni mai tsarki,Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila,Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.

3. Ubangiji ya ce wa Isra'ila,“Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru,Sa'an nan na sa ya faru ba labari!

4. Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne,Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.

5. Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku,Na hurta abubuwa tun kafin su faru,Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su,Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.

6. “Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu,Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce.Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo,Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.

Karanta cikakken babi Ish 48