Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 47:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari!Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!

3. Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma,A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa.Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”

4. Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya fanshe mu,Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!

5. Ubangiji ya ce wa Babila,“Ki zauna shiru a cikin duhu,Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al'ummai ba!

6. Na yi fushi da mutanena,Na maishe su kamar su ba nawa ba ne.Na sa su a ƙarƙashin ikonki,Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba,Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.

7. Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin,Ba ki ɗauki waɗannan al'amura a zuci ba,Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.

Karanta cikakken babi Ish 47