Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 47:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki,Ki zauna a ƙasa cikin ƙura.Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba!Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi!Ke baiwa ce yanzu!

2. Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari!Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!

3. Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma,A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa.Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”

4. Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya fanshe mu,Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!

5. Ubangiji ya ce wa Babila,“Ki zauna shiru a cikin duhu,Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al'ummai ba!

Karanta cikakken babi Ish 47