Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 44:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ka saurara yanzu, ya Isra'ila, bawana,Zaɓaɓɓun mutanena, zuriyar Yakubu,

2. Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku,Tun farko, na taimake ku.Kada ku ji tsoro, ku bayina ne,Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.

3. “Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi,In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada.Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku,In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.

4. Za su yi kumari kamar ciyawar da ta sami ruwa sosai,Kamar itatuwan wardi a gefen rafuffukan ruwa mai gudu.

5. “Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila.Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa,Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”

Karanta cikakken babi Ish 44