Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 40:25-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki?Ko akwai wani mai kama da shi?

26. Ka dubi sararin sama a bisa!Wane ne ya halicci taurarin da kake gani?Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji,Ya sani ko su guda nawa ne,Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa!Ikonsa da girma yake,Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!

27. Isra'ila, me ya sa kake gunaguni,Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba,Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka?

28. Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?Ubangiji Madawwamin Allah ne?Ya halicci dukkan duniya.Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba.Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.

29. Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.

30. Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala,Samari sukan siƙe su fāɗi,

31. Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimakoZa su ji an sabunta ƙarfinsu.Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa,Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba,Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.

Karanta cikakken babi Ish 40