Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 39:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe dukan abin da yake a fādarka, da dukan abin da kakanninka suka tara har ya zuwa yau, zuwa ƙasar Babila. Ba abin da za a rage.

7. Waɗansu daga cikin zuriyarka ta kanka, za a tafi da su a maishe su babani domin su yi hidima a fādar Sarkin Babila.’ ”

8. Da sarki Hezekiya ya gane, wannan zai faru ne a bayansa, wato a zamaninsa ba kome sai lafiya, sai ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

Karanta cikakken babi Ish 39