Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 36:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”

7. Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa'an nan ya faɗa wa jama'ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum.

8. Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su!

9. Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai!

10. Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”

11. Sa'an nan sai Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka ce wa shugaba na Assuriya, “Ka yi mana magana da harshen Aramiyanci, muna jinsa. Kada ka yi da Ibrananci, dukan jama'ar da suke a kan garu suna saurare.”

12. Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama'ar da suke a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”

13. Sa'an nan ya tsaya ya ta da murya da harshen Ibrananci, ya ce, “Ku saurara ga abin da Sarkin Assuriya yake faɗa muku.

Karanta cikakken babi Ish 36