Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 36:15-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku.

16. Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci 'ya'yan inabi daga gonakinku, da 'ya'yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku,

17. har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.

18. Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al'ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?

19. Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba?

20. A yaushe ko gunki ɗaya na dukan waɗannan ƙasashe ya taɓa ceton ƙasarsa daga babban sarkinmu? To, yanzu me ya sa kuke tsammani Ubangiji zai ceci Urushalima?”

Karanta cikakken babi Ish 36