Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 32:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu.

8. Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.

9. Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

10. Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara.

11. Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12. Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi,

13. ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama'ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā.

14. Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.

15. Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.

16. A ko'ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya.

17. Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.

Karanta cikakken babi Ish 32