Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 32:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya.

2. Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

3. Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama'a.

4. Za su zama masu haƙuri sosai, za su yi kome da haziƙanci, za su kuma faɗi abin da suke nufi.

5. Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci.

6. Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.

7. Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu.

8. Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.

9. Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

10. Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara.

11. Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

Karanta cikakken babi Ish 32