Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 30:29-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Amma ku, jama'ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra'ila.

30. Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

31. Assuriyawa za su firgita sa'ad da suka ji muryar Allah, suka kuma ji irin zafin hukuncinsa.

32. Sa'ad da Ubangiji ya miƙa sandan hukuncinsa ya yi ta bugun Assuriyawa, jama'arsa kuwa za su yi ta kaɗa ganguna da garayu, su yi murna!

33. An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.

Karanta cikakken babi Ish 30