Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 3:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da 'yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa.

4. Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama'ar.

5. Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.

6. Lokaci yana zuwa sa'ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”

7. Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”

8. Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.

9. Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.

10. Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata.

11. Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.

Karanta cikakken babi Ish 3