Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 29:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.

18. A wannan rana, kurame za su ji sa'ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.

19. Matalauta da masu tawali'u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya bayar.

20. Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.

21. Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.

22. Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya fanshi Ibrahim daga wahala, ya ce, “Jama'ata, ba za a ƙara kunyatar da ku ba, fuskokinku ba za su ƙara yanƙwanewa don kunya ba.

23. Za ku ga 'ya'yan da zan ba ku, sa'an nan ne za ku tabbatar, cewa ni ne Allah Mai Tsarki na Isra'ila. Za ku girmama ni, ku yi tsorona.

24. Wawaye za su koya su gane, waɗanda a kullum sai gunaguni suke yi, za su yi murna su koya.”

Karanta cikakken babi Ish 29